‘Yan Bindiga sun kashe mutum 3 da sace 22 a Jihar Kaduna

0
87

‘Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu mutane 22 da suka hada da manoma a wasu kauyukan karamar hukumar Birnin-Gwari ta jihar Kaduna.

Shugaban kungiyar ci gaban masarautar Birnin-Gwari (BEPU), Ishaq Usman Kasai, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce a ranar Asabar, 24 ga Satumba, 2022 da misalin karfe 7:30 na yamma, ‘yan bindigar sun kai hari Hayin Gada da ke unguwar Damari a gundumar Kazage, inda suka kashe mutum biyu wato; Sanusi Zubairu da Kabiru Zubairu da yni garkuwa da mutane 12 tare da wawashe kayan wasu shaguna a unguwar a yayin harin.

“A ranar Asabar din nan ne wasu ‘yan bindiga suka kashe mutum 1 tare da yin garkuwa da mutane 6 a FARM CENTER da ke kusa da titin Birnin-Gwari/Kaduna sun yi garkuwa da wasu 4 a Dajin Jangali tare da kwace babura 3 (Bajaj Model) na manoma a unguwar Kamfanin Doka.”

BEPU ya lura da tsananin damuwa da yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da mamaye al’ummomi daban-daban da wawure kayayyaki a shaguna da fuskantar kalubale.

Shugaban kungiyar ta BEPU ya ce kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ci gaba da yin kira ga hukumomin da abin ya shafa da su kara kaimi wajen yakar ayyukan ta’addanci a karamar hukumar Birnin-Gwari musamman a wannan lokaci na noma.

 

LEADERSHIP