Iyalan marigayi Sheikh Aisami sun nuna rashin jin dadi akan rashin hukunta sojojin da ake zargi da kashe shi

0
40

Iyalan malamin addinin Musuluncin nan da aka yi wa kisan gilla a jihar Yobe da ke arewacin Najeriya, Sheikh Goni Aisami, sun bayyana damuwarsu ga yadda suka ce har yanzu ba a gurfanar da wadanda ake zargi da kashe shi a gaban kotu ba kusan kwana hamsin da faruwar lamarin.

Wani soja ne da malamin ya rage wa hanya ake zargi da harbe shi domin ya sace motarsa yayin da malamin ke kan hanya daga Kano zuwa Gashua. Sai dai hukumomi sun ce nan ba da jimawa ba za a soma shari’ar gadan-gadan.

Ɗaya daga cikin iyalan marigayin ya ce ba su ga dalilin da zai sa a yi tsaiko wajen hukunta waɗanda ake zargi. Abdullahi Goni Aisami ya ce sun shiga tashin hankali saboda rashin jin wata hujja daga hukumomi kan abin da ya sa aka ƙi hukunta mutanen.

“Muna cikin baƙin ciki da takaici, su daga ɓangaren matan malam, hankalinsu ya fi na kowa tashi saboda suna ganin kamar an ma ƙi yin hukuncin ne haka kawai,” in ji shi.

Daga ɓangaren hukuma kuwa, kakakin rundunar ‘ƴan sanda na jihar Yobe, DSP Dungus Abdulkareem ya ce bayan sun gama bincike suka tura wa hukumar shari’a ta jihar domin tabbatar da cewa an gurfanar da waɗannan sojoji guda biyu gaban kotu.

“An yi nasarar haka, inda ranar 19 ga watan Satumba aka gabatar da su a gaban kotu, kuma kwamishina da kansa ya zama lauya mai gabatar da ƙara na gwamnati,” a cewarsa.

“Ya gabatar da hujjojinsa da shaidunsa gaba ɗaya a gaban kotu inda waɗanda ake zargi suka ce su ba su da laifi, sannan aka tsaya daga nan aka rufe ƙarar, za a sake sauraron shari’ar a zama na biyu.”

DSP Dungus ya ƙara da cewa lokacin da aka yi zaman shari’ar kotunan Najeriya suna hutu, kuma “muna tunanin idan sun dawo hutu, za su gaya mana ranar da za a sake dawo da sojojin zuwa kotun.

BBCHAUSA