Gwamnatin Legas ta yi barazanar kama wa da gurfanar da masu siyarda kaya a gefen hanya

0
40

Kwamitin Kar-ta-kwana na jihar Legas ya gargaɗi masu saide-saide da ke kan titin Oshodi da ke baje kolin kayayyakinsu a gefen hanya cewa za ta kama su.

Shugaban kwamitin, Shola Jejeloye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labarai da hulda da jama’a, Abdulraheem Gbadeyan, ya fitar a jiya Laraba.

Jejeloye ya lura cewa an gargadi ‘yan kasuwa da masu motocin haya a farkon shekarar nan, bayan da gwamnati ta samar da isassun wuraren kasuwanci kantuna, da rukunin kantuna na sojojin ƙasa na Nijeriya.

Ya ce, “Mun gudanar da atisayen tursasa wa masu saide-saide da su dena a ranar 9 ga watan Maris na wannan shekara inda ‘yan kasuwar suka kama wasu kayayyaki, sannan aka kama motoci daga hannun wasu direbobin bas ɗin haya amma mun tausaya wa ƴan kasuwar da wasu direbobin, wadanda suka sayi wasu daga cikin kayayyakin ta hanyar bashi tare da alkawarin ba za su sake komawa bakin hanya ba.

“Abin takaici, sai gashi sun dawo kan hanya kwata-kwata, amma a wannan karon duk wanda aka kama yana baje kolin kaya a bakin titi hukumar za ta kama shi kuma ta gurfanar da shi a gaban kotu.

“Masu motocin haya ma wadanda aka samu da rashin da’a da rashin bin ka’idojin zirga-zirgar ababen hawa za a kama su kuma a kama motocin su idan ba su daina ba.”

DailyNigeria