HomeLabaraiPDP ta maka gwamnan Kwara a kotu kan zargin amfani da takardun...

PDP ta maka gwamnan Kwara a kotu kan zargin amfani da takardun bogi

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

An gurfanar da Gwamnan Jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasaq a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, bisa zarginsa da yin amfani da takardar shaidar kammala karatu ta WAEC ta bogi wajen tsayawa takarar gwamna a zaben 2023 a Jihar.

A karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kansa, an bukaci babbar kotun tarayya da ta haramta wa gwamna da jam’iyyar APC shiga zaben gwamna na shekara mai zuwa.

Sabuwar karar mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/22 ta shigar da kara ne a madadin PDP ta hannun wani babban lauyan Nijeriya, SAN, Cif Paul Erokoro, tare da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), Abdulrahman Abdulrasaq da APC, a matsayin wanda ake tuhuma na 1 zuwa na 3.

An bukaci kotun da ta yi amfani da sashe na 171 da 285 na kundin tsarin mulkin kasar nan na 1999 da kuma sashe na 29 na dokar zabe domin soke shirin da gwamnan zai yi a zabe mai zuwa.

PDP ta kuma roki kotun da ta tilasta wa INEC da ta cire gwamnan da APC daga jerin sunayen ‘yan takara da jam’iyyu da aka tantance.

Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa takardar shaidar kammala karatu ta WAEC da gwamna ya mika ta hannun jam’iyyar APC domin ta taimaka masa wajen neman ilimi kamar yadda sashe na 177 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999 ya tanada ta jabu ce.

A halin da ake ciki, mai shari’a Inyang Edem Ekwo ya sanya ranar 28 ga watan Oktoba domin sauraren karar.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories