Dan takarar Sanata a jihar Yobe ta Arewa Machina ya sake samun nasara a kotu

0
58

Tsohon dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa a Jihar Yobe, Abubakar Abubakar Jinjiri, ya janye karar da ya shigar a kan dan takarar kujerar sanata na jam’iyyar APC, Bashir Sheriff Machina da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da kuma jam’iyyar APC.

Sanata Jinjiri, ta bakin lauyansa, Barista Usman Lukman Nuhu, ya shaida wa mai shari’a Fadima Aminu ta babbar kotun tarayya da ke zamanta a Damaturu, babban birnin Jihar Yobe, cewa an shigar da sanarwar dakatar da wadanda ake kara a kan lamarin.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne jim kadan bayan da aka bukaci a saurari karar a ranar Laraba.

Barista Nuhu ya sanar da cewar Jinjiri da ya janye karar sannan ya roki kotu da ta dakatar da shari’ar tare da bayar da umarnin soke karar.

Lauyan Machina, Barista Mohammed Ngumurumi wanda ya rike da takaitaccen bayanin Ibrahim Bawa, SAN, ya roki kotun da ta yi watsi da karar maimakon ta soke ta.

Sauran wadanda ake tuhuma kuma ba su yi adawa da sanarwar janye mai karar ba.

A hukuncin da ta yanke, mai shari’a Fadima Aminu ta bayyana cewa Jinjiri na da damar shigar da sanarwar janyewar kararsa.

Ta ce sanarwar dakatarwar ta na nan daram saboda haka ta yi watsi da karar kamar yadda lauyan Machina ya bukata.

A ranar 17 ga watan Yuni ne Jinjiri ya garzaya babbar kotun tarayya da ke Damaturu tare da gabatar da karar gabanin zabe yana kalubalantar takarar Bashir Machina wanda ya lashe zaben fidda gwanin dan takarar Sanata na jam’iyyar APC na mazabar Yobe ta Arewa a ranar 2 ga watan Mayu.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa a makonnin da suka gabata ne kotun ta ayyana Machina a matsayin wanda ya cancanta a matsayin zababben dan takarar kujerar Sanatan Yobe ta Arewa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2023, wanda hakan ya kawo karshen cece-kuce da suka dabaibaye jam’iyyar APC a Yobe ta Arewa.