Yana da kyau matasa su rika shiga harkar kudaden Crypto – Farfesa Aliyu Jibiya

0
69

Farfesa Aliyu Abdullahi Jibiya, daga Jami’ar Bayero ta Kano, ya yi kira ga matasa da su ci gajiyar kasuwanci da kudaden Intanet da suka mamaye duniya a wannan lokacin.

Farfesa Jibiya ya bayyana cewar kudin kasuwanci na Intanet mai suna ZUGACOIN daya ne daga cikin wadan da suka fi shahara a harkar kudin Intanet a duniya.

Aliyu Jibiya, ya bayyana haka ne a yayin tattaunwa da Jaridar Daily Post, a yayin bikin karrama shugaban gidauniyar SAMZUGA, wanda ya shahara wajen hadahadar kasuwanci da kudaden Intanet.

Jibiya ya bayyana cewa, “Archbishop Farfesa SamZuga wanda yake jami’in diflomasiyya a tsarin ‘INTERNATIONAL SOCIETY OF DIPLOMATS AND GLOBAL EMISSARY COUNCIL’, wanda shi ne shugaban kula da sasheb tattalin arziki na farko a tsarin IT na duniya.”

“Samzuga na cikin farko-farko a fannin tattalin arziki a tsarin kudin Intanet na duniya, kuma shi ne farkon wanda ya kafa cibiyar hada-hadar kasuwanci a Afirka.”

Farfesa Jibiya, ya kuma kara da cewa, “Samzuga wanda ya samar da kudin ZUGACOIN, na daya daga cikin kamfanoni uku da suka fi shahara a harkar kudin Intanet a tsakanin ‘yan Nijeriya da ke a wasu kasashen duniya.”

“Archibishop Farfesa Sam Zuga, limamin coci ne a Nijeriya da ke zaune a Dubai, dan kasuwa ne mai taimakon jama’a, ya samu lambar yabo ta digirin girmamawa daga jami’o’i daban-daban a duniya, ciki har da wasu jami’o’in kasar Amurka.”

“Haka kuma, Archbishop Farfesa SamZuga, mamba ne a kungiyar ‘yan kasuwa ta Dubai, kuma dan Nijeriya na biyu da ya karbi lambar yabo daban-daban a fannin zaman lafiya a kokarinsa na samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin al’umma a ciki da wajen Nijeriya, haka kuma, an taba ba shi lambar yabo ta Jakadan Majalisar Dinkin Duniya kan zaman lafiya.

“Archbishop Farfesa SamZuga, yana da lasisi a Dubai wanda ke ba shi damar shigo da zinari daga sassan duniya zuwa Dubai, kuma shi ne ya samar cibiyar kasuwanci ta Intanet don kawo shirye-shiryen sauyin yanayi wanda aka sanar a hukumance a taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya, wannan manufar ita ce kawar da radadin matsin lamba na rayuwa ga masu karamin karfi.”

A jawabinsa yayin karbar lambar yabo, Farfesa Mkpa Ogoh Mkpa, wanda ya wakilci Archbishop Farfesa Sam Zuga, ya gode wa Ubangiji Madaukakin Sarki da gaisuwa ta musamman bisa karramawar da aka yi masa, ya kuma tabbatar da cewa Archbishop Farfesa Sam zai ci gaba da yin iya kokarinsa, zai kara himma wajen samar da sabbin abubuwa don ciyar da al’umma gaba kamar yadda ya saba.