HomeLabaraiMajalisar dokokin Delta ta amince wa Okowa karbo bashin naira biliyan 4

Majalisar dokokin Delta ta amince wa Okowa karbo bashin naira biliyan 4

Date:

Related stories

Sarkin Dutse Nuhu Sunusi ya rasu

Allah ya yi wa Sarkin Dutse Alhaji Dr. Nuhu...

Shin ko kunsan tsibirin da aka hana kowa zuwa a duniya ?

Shi wannan guri Mai suna North Sentinel Island an...

Mayakan ISWAP sun raba wa fasinjoji dubu dari-dari

Mayakan ISWAP sun rarraba wa fasinjoji da dama Naira...

Ya kamata mutane su yi amfani da kwanaki 10 wajen mayar da tsofaffin kudin su banki – Sanusi

Sarkin Kano murabus kuma Khalifan Tijaniyya, Sanusi Lamido Sanusi,...

‘Yan sanda sun bankado maboyar ‘yan bindiga, sun cafke mutum 6 a Nasarawa

Rundunar ‘yansandan Jihar Nasarawa ta ce ta kai farmaki...

Majalisar Dokokin Delta ta amince wa Gwmna Ifeanyi Okowa karbo bashin Naira Biliyan hudu domin aiwatar da shirin samar da gidaje ga jama’a.

Wannan ya biyo bayan kudirin da Shugaban Masu Rinjaye na majalisar, Chif Ferguson Onwo ya gabatar a zamanta na ranar Talata, inda ya samu goyon bayan Mataimakin Shugaban Majalisar, Christofa.

Majalisar ta kuma amince da wata bukatar Gwamnan na karbo wani bashin na Naira biliyan 1.2 daga Bankin Globus domin samar da kudaden aiwatar da shirin bai daya na Hukumar Samar da Ilimin Matakin Farko (UBEC) a jihar.

A wasikar da ya mika wa majalisar, Gwamnan ya ce: “Bisa la’akari da karancin kudaden da jihar mu ke fama da shi yanzu, ya zama dole mu nemo hanyoyin da za mu ci gajiyar shirin samar da ilimin bai daya na matakin farko na kasa.

“Cikin ikon Allah Bankin Globus ya nuna sha’awar samar wa jihar kudaden da ta ke bukata.

“Bayan ba mu takardar tayin da ke nuna sharuddan da suka dace da jihar, bisa la’akari da yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

“Za kuma mu biya lamunin ne a shekara guda”, in ji Gwamnan a wasikar da ya aika wa majalisar.

Subscribe

- Never miss a story with notifications

- Gain full access to our premium content

- Browse free from up to 5 devices at once

Latest stories