Emefiele ya tabbatarmin ba za a cire rubutun ajami ajikin naira ba – Sanusi

0
40

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya tabbatar da cewa ba za a cire rubutun Ajami a jikin kudin da ake shirin sake wa fasalin ba.

Sanusi ya yi ikirarin cewa Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ba shi tabbacin cewar ba za a cire rubutun Larabci ba daga jikin takardun da aka sake wa fasalin ba.

A makon da ya gabata ne CBN ya bayyana cewa zai sake fasalin takardun kudi na N100, N200, da N1000, wanda zai fara aiki a ranar 5 ga Disamba, 2022.

Ra’ayoyi mabanbanta sun yi maraba da sanarwar CBN yayin da wasu malaman addinin Musulunci suka yi zargin cewa sake fasalin Naira wani shiri ne na cire rubutun Ajami.

A yayin da malaman addinin Islama ke zargin wasu ‘yan Nijeriya sun bukaci babban bankin kasar da ya cire rubutun daga jikin kudin da aka sake wa fasali.

Da yake mayar da martani, Sanusi ya bukaci shugabannin addinin Musulunci da su kwantar da hankalinsu kan lamari.

“An yi ta cece-kuce game da sauya wasu takardun Naira. Na ji malamai daban-daban suna sharhi, wasu na nuni da cewa za a cire Ajami a kan kudin Naira.

“Tun da batun ya taso, mun tattauna da wasu mutane a babban bankin kasar nan, kuma sun tabbatar min da cewa babu wannan shiri.

“Lokacin da wannan mummunar fahimta ta yadu, na yi magana da Gwamnan CBN da kansa, kuma ya tabbatar min da cewa babu wani shiri ko kadan na cire Ajami.

“Don haka, ina so in yi kira ga malaman addinin Musulunci da su daina aiki da rahotannin da ba su da tushe,” kamar yadda ya shaida wa manema labarai.