Ronaldo zai jagoranci tawagar Portugal a gasar kofin duniyia

0
203

Cristiano Ronaldo zai fafata a gasar cin kofin duniya a karo na 5 kenan a rayuwarsa ta kwallon kafa, bayan da Portugal ta sanya shi a  cikin tawagar da za ta wakilci kasar a gasar da za  a yi a Qatar.

Da ma an sa ran a sanya dan wasan mai shekaru 37, wanda shi ne dan kwallon da ya fi cin kwallaye a wasan tamola a wasannin kasa da kasa da kwallaye 117 a cikin tawagar da za ta wakilci Portugal, sai dai ba ya cikin ganiyarsa a daidai wannan lokaci.

Kwallaye 3 ne kawai Ronaldo ya ci daga wasanni 16 da ya buga a dukkan gasa, kuma wasannin gasar Firimiyar Ingila 4 ne kawai aka fara da shi a wannan kaka.

Tun da farko tsohon dan wasan na Real Madrid da Juventus ya mika bukatar barin United a farkon wannan kaka, amma abin ya fasakara, duba da cewa babu wata kungiya da ta nuna sha’awar aiki da shi.

Sai da ma kocin United Erik Ten Hag ya ajiye shi a benchi bayan da ya ki yin wasa a lokacin da aka sanya shi daga baya a Oktoba.