An sace mataimakin daraktan IAR da ke Zariya

0
143
Maharan da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Mataimakin Daraktan Cibiyar Bincike kan Ayyukan Gona (IAR) ta Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zariya, Farfesa Ado Yusuf.

Majiyar iyalan mutumin ta shaida wa wakilinmu cewa a ranar Juma’ar da ta gabata da yamma, Farfesan ya tafi wani kanti da nufin sayen burodi kamar yadda ya saba, amma tun daga wannan lokacin ba a sake jin duriyarsa ba.

Hakan ya sa aka je shagon inda aka ci karo da motarsa a ajiye a bakin katafaren kantin, amma kuma duk binciken da aka yi a babu Farfesan.

Idan za a iya tunawa, ko a mako biyu da suka gabata, ’yan bindigar sun sace matar Mataimakin Daraktan a gidansu da ke Zangon Shanu a unguwar Samaru da ke Zariya cikin talatainin dare.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, wani dan uwan Farfesan, Abdusalam Yusuf ya ce bayan da suka neme shi suka rasa, sun ziyarci kantin sayar da burodin inda suka tarar da motarshi a ajiye.

Daga nan, Yusuf ya ce sun bukaci a sanya masu faifan kyamarar nadar bayanai ta CCTV ta shagon, inda suka ga shigar Farfesan da fitar shi shagon, duka shi kadai ba tare da wani ba.

“Hakan ta sa muka yi ta kiran lambobin wayoyinsa, inda muke tunanin ko zai je amma hakar mu bata cim ma ruwa ba.

“Don haka na garzaya ofishin ’yan sanda na sanar da su abin da yake wakana. Domin muna tsoro ko wadanda suka sace matarsa ne kuma suka dawo suka sace shi, shi ma,” inji Yusuf.

Aminiya ta ruwaito cewa Farfesa Ado Yusuf yana cikin mahalarta taron da aka gudanar a cibiyar da yake jagoranci akan noman audugu a ranar Alhamis, kafin ranar Juma’a kuma a neme shi a rasa.

Sai dai duk kokarin da Aminiya ta yi don jin ta bakin hukumomin jami’ar ta Ahmadu Bello da ke Zariya a kan lamarin sun ki cewa komai har zuwa lokacin hada wannan rahoton.