Amurka ta sanya wa yariman Saudiyya rigar kariya kan kisan Khashoggi

0
60

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar da wata kotun ƙasar cewa yariman Saudiyya Mohammed bin Salman yana da rigar kariya saboda sabon matsayinsa na firaiministan Saudi Arabia.

A saboda haka Amurkar ta ce ba za a iya hukunta shi a sharia’ar da budurwar ɗan jaridar nan da aka kashe Jamal Khashoggi ta shigar game da kisan saurayin nata ba.

Khashoggi, shahararren mai sukar gidan sarautar Saudiyya, an kashe shi ne a ofishin jakadancin Saudiyya da ke ƙasar Turkiyya a cikin watan Oktoba na shekarar 2018.

Jami’an tattara bayanan tsaron sirri na Amurka sun ce sun yi amannar yarima bin Salman ne ya bayar da izinin kisan.

Budurwar Kashoggi ta ce wannan matsaya da hukumomin Amurka suka ɗauka tamkar bi-ta da ƙulli ne a kan mamacin.

Matar, mai suna Hatiz Cengiz, tare da wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Arab World Now sun shigar da ƙara ne suna neman diyya daga yariman na Saudiyya bisa kisan Jamal Khashoggi.