Buhari zai bude aikin tono man fetur a Bauchi da Gombe

0
61

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da aikin tono man fetur a jihohin Bauchi da Gombe.

An dai gano tarin arzikin man fetur a jihohin biyu shekaru biyu da suka gabata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito ƙaramin ministan man fetur na ƙasar Timipre Sylva, na cewa ”Za a gudanar da bikin fara tono man ranar Talata 22 ga watan Nuwamba Inda shugaba Buhari tare da wasu daga cikin ministocinsa za su halarta”

A shekarar 2016 ne kamfanin mai na ƙasar NNPC ya ƙaddamar da aikin binciko man fetur a arewacin ƙasar, abin da ya kai ga gano ɗimbim albarkatun man fetur ɗin a jihohin Bauchi da Gombe da Borno da kuma jihar Niger.

A yayin da ƙasar ke dogara da man da ake tonowa daga yankin Niger Delta, Wannan shi ne karo na farko da za a fara tono man a yankin arewacin ƙasar, bayan da rikicin Boko Haram ya hana yunƙurin tono man a jihar Borno.