Buhari ya bayyana wadanda ke da hannu a ta’addacin Boko Haram

1
62
Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wasu kungiyoyin kasa da kasa ne ke kai hare-haren Boko Haram a kasar.

Buhari ya yi wannan jawabi ne a lokacin wata liyafar cin abincin shugaban kasa da gwamnatin jihar Kano ta shirya masa a ziyarar aiki ta yini daya.

“Lokacin da muka hau mulki a shekarar 2015, Boko Haram sun mamaye kananan hukumomi 13 cikin 17 na jihar Borno domin hudu ne kawai ke gwamnati ke rike dasu a lokacin.

Buhari ya shaida wa taron cewa yana zargin akwai wata kungiyar kasa da kasa da ke son ruguza Najeriya, inda ya kara da cewa, “Idan ba haka ba, ta yaya Boko (ilimin zamani ) zai zama Haram?

“Sun zo ne domin hana mu ci gaban damu ke samu a tafkin Chadi.

“Amma mun yi nasarar nunawa ‘yan Najeriya da sauran kasashen duniya cewa muna da albarkatun kasa da yawa a can,” in ji shi.

“Dole ne mu kara yin addu’a kuma mu gode wa Allah, za mu yi yakin neman kasarmu daga kungiyoyin kasa da kasa da ke kokarin ruguza Najeriya.

“Mun yi sa’a sosai cewa wannan gwamnati ta wannan bangaren da kuma Gwamna Zulum na Jihar Borno, wanda shima ya yi matukar kokari sosai.

“Na yi matukar farin ciki da ‘yan Najeriya sun nuna min goyon baya.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here