Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), Nasir Kwarra, ya ce matsalar tsaro ba za ta hana shi gudanar da aikin na bana a Dajin Sambisa ba.
Saboda a cewarsa, wajibi ne su ma mazauna yankin a kidaya.
Ya ce, an riga an kididdige gidaje a dajin a lokacin da aka gudanar da shirin tantance gidaje, don haka babu abin da zai hana shi gudanar da kidayar a wasu sassan kasar.
Kwarra ya bayyana haka ne a wajen taron auna ayyukan gwamnatin Buhari karo 24 ranar Alhamis a Abuja.
Ya kara da cewa, kawo yanzu kudi sama da N100bn aka kashe wajen shirye-shiryen kidayar ta bana.
Da yake jawabi, Ministan Yada Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce shirin kidaya na wannan karon zai kafa sabon tarihi a Najeriya saboda kyakkyawan shirin da gwamnati ta yi.