‘Yan sanda sun cafke mutum 50 kan satar kaya lokacin da gobara ke cin kasuwar Monday market a Borno

0
55

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta gurfanar da wasu mutane 50 da ake zargi da wawure kayayyaki iri daban-daban na ‘yan kasuwar Monday da ke maiduguri yayin wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Lahadi.

 

Wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, ASP Sani Kamilu Shatambay, ya fitar a ranar Laraba ga manema labarai a Maiduguri, ta ce a ranar 26 ga watan Fabrairun 2023, an samu labarin mummunar gobara da ta tashi a babbar kasuwar Monday da ke Maiduguri, babban birnin jihar.

 

Ya ce a lokacin da rundunar ‘yan sandan ta samu labarin faruwar lamarin, ta tura jami’anta zuwa wajen da lamarin ya faru domin dakile satar dukiyar jama’a, jami’an kashe gobarar sun kwashe sama da sa’o’i takwas kafin kashe gobarar.

Ya ce, a wannan lokacin yayin da ake kokarin kashe gobarar, jami’an ‘yansanda sun cafke sama da mutane 50 dauke da kayayyakin jama’a da suka sace, inda ya ce, barayin suna hannun ‘yan sanda ana gudanar da bincike, za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here