Kamfanin siminti na Dangote ya samu gagarumar riba da bunkasa a 2022

0
51

Kamfanin sarrafa siminti na Dangote, ya kamala hada-hadarsa ta shekarar 2022 a cikin nasara, inda wannan nasarra ta sa ta kasance biyo bayan gudanar da kyakywan shugabanci da ake ci gaba da yi a masana’antar.

Masu zuba jari a fannin kasuwancin na simitin sun ci gaba da zuba jarinsu domin su amfana da ribar da ake samu daga kamfanin a duk shekara.

Bugu da kari, kamfanin ya zamo a kan gaba a kamfanin hada-hadar a musayar kudade na kasar nan wato (NGD), inda ya ci gaba da biyan ribar da samu daga ga wadanda suka zuba jarin su a kamfanin na sarrafa simintin.
Kamfanin ya kuma kasance a kan gaba a nahiyar Afirka wajen sarrafa ingantaccen siminti.

An wallafa sakamakon kokarin kamfanin ne ya yi ne a ranar 31 ga watan Disambar 2022, inda hakan ya nuna kudin shigar da kamfanin ya samu a shekarar ta 2022, sun karu zuwa kashi 16.96 a cikin dari daga cikin naira tiriliyan 1.383 a 2021 zuwa naira tiriliyan 1.618 a 2022.

Bisa ga fashin bakin da aka yi kan kudin sun nuna cewa, a cikin Nijeriya kawai, an sayar da simintin da ya kai na naira tiriliyan 1.172 daga naira biliyan 956.96.

Har ila yau, kudin sarrafa simintin wanda aka sayar ya karu da kashi 20.3 a cikin dari daga naira biliyan 551.019 zuwa naira biliyan 662.89, inda kuma gundarin ribar da aka samu ta karu zuwa naira biliyan 955.433, inda wannan ya kai kashi 14.75 a cikin dari daga naira biliyan 832.618 a 2021.

Hakazalika, kudaden tafiyar da shugabancin kamfanin sun karu daga naira biliyan 64.349 zuwa naira biliyan 79.879. Sauran kudaden shiga kuwa, sun ragu zuwa naira biliyan 5.333 daga naira biliyan 6.221, inda kuma kudaden shiga suka karu zuwa naira biliyan 38.715 daga naira biliyan 20.765, inda hakan ya nuna kamfanin ya samu karin kashi 86.44 a cikin dari.

Sauran cajin kudade sun karu zuwa kashi 98.41 a cikin dari daga naira biliyan 65.707 a of 2021 zuwa naira biliyan 130.37.
Kamfanin ya biya harajin da ya kai na naira biliyan 52.002, inda kuma ya samu riba bayan ya biya harajin naira biliyan 382.311 ,inda kudin shigar suka karu zuwa naira 22.27 daga naira 21.24.

Tsarin bayar da riba da daraktocin kamfanin suka fito da shi, ya yi dai-dai da kudin shiga da kamfanin yake samu ,inda kuma suke ci gaba da bin shirin tafiyar da kamfanin tare da fadada ayyukan kamfanin.

A hada-hadar kudi ta kamfanin a 2022 kamfanin ya dora rabar da riba akan naira 20.00 na ko wacce shiya daya, musamman domin biyan wadanda suka zuba jarin kuma sunyyen su suka kasance an yi masu rijista kafin a rufe hada-hadar kasuwancin a ranar 30 ga watan Maris na 2023.

Bugu da kari, a bisa kokarin mahukuntan kamfanin don su dakile kashe kudade barkatai, musamman na makamashi, kamfanin ya mayar da hankali wajen yin amfani da tsarin samar da makamashi ga kamfanin sarrafa simintin na Dangote da ke a Obajana da wanda yake a Ibese ,inda wannan ya kai kashi 7.5 a cikin dari a watan Disambar 2022.

Masu yin fashin baki a kamfanin hada-hadar kudade na Cordros Securities, sun bayyana jin dadin su kan kokarin na kamfanin simintin na Dangote, musamman akan jajircewar san a samun riba duk da kalubalen da ya ke fuskatna wajen gudanar da ayyukan sa a daukacin fadin kasar nan da kuma a nahiyar Afirka.

A cewar kamfanin, duk da tsadar farashin simintin, yana fatan kamfanin ci gaba da jajirce wa da yin aiki a 2023, mussaman don ya ci gaba da rike kambun sa wajen sarrafa simintin.

Shi ma Kamfanin Coronation Asset Management ya sanar da cewa, mun samu kwarin guiwa akan kamfanin na Dangote ganin yadda ya yi amfani da hauhawan farashin na simintin, amma ya samar da wadataccen shi a kasar nan da kuma a kasuwannin Afirka. A bisa tarihin kamfanin, a zango na hudu na shekarar yawan simitin da ka sarrafa, ya karu inda kamfanin na Coronation Asset Management ya danganta kokarin da kamfanin simimtin na Dangote ya yi a zago na hudu a 2022.

Kamfanin na Coronation Asset Management ya ci gaba da cewa, bisa tsaka-tsaki, muna sa ran farashin ya ci gaba da hawa har zuwa lokacin da za a kamala gyare-gyaren da ake yi a kamfanin na sarrafa simintin.

Ya kuma nuna damuwar sa akan yawan rashin samun wuta a rkunonin kamfanin na Dangote da ke kasasehn Kongo da Senigal, ganin cewa, ana ci gaba da gudanar da ayyukan gyare-gyare masana’antun.

Bugu da kari, Kamfanin na Coronation Asset Management ya kuma nuna damuwar sa kan tsadar gudnar da ayyukan na kamfanin Dangote saboda kalubalen makamashi da na sauran kayan aiki.

Hakazalika, a kwanan baya kamfanin sarrafa simitin na Dangote ya sanar da cewa, ya na ci gaba da kirkiro da hanyoyin samun masu zuba jari a kamfanin na sarrafa simitin sama da kokarin sa rabar da riba ga wadanda suka zuba jarin su a kamfanin.

A cewar kamfanin na Dangote, yana son ganin kamfanin ya kara samun karbuwa a gun masu zuba jari a cikin gajere da kuma dogon zango, inda kamfanin ya kara da cewa, ya mayar da hankali wajen bin ka’idoji da dokokin da suka da ce don ci gaba da gudanar da ayyukan sa a cikin nasara.

“Muna ci gaba da mayar da hankali akan daukacin matakan kasuwancin mu da kuma tabbatar wa da wadanda suka zuba jarin su a kamfanin sanin ci gaba da tsarin mu.”
Shugaban kamfanin Aliko Dangote a taron shekara-shekara na 2021 ya sanar da cewa, “Kamfanin ya shafe shekaru yana samun bunkasa a fannoni da ban da ban na gudanar da ayyukan sa.”

Aliko Dangote ya ci gaba da cewa, yawan simitin da muke sarrafa way a kai kimanin 30Mta, inda kuma rubanya zuwa 51.6Mta, inda ya ce, muna kuma fitar da simitin da muka sarrafa zuwa daukacin kasashen da ke a cikin nahiyar Afirka.

A cewarsa, duk da kalubalen da aka fuskanta a fadin duniya, a cikin shekaru buty da suka wuce, mun ci gaba da jure wa wajen aiwatar da ayyukan mu ba bu kakkauta wa.

Ya sanar da cewa, kamfanin siminti na Dangote har zuwa yau, ya ci gaba da zamo wa akan gaba wajen sarrafa simiti a Afirka, inda ya kara da cewa, “muna da kwarin guiwa ganin muna isassuun kayan aiki don ci gaba da gudanar da ayyukn mu.”
Kamfanin na Dangote na da karfin sarrafa simitin da ya kai yawan tan miliyan 51.6 a duk shekara tare da fitar da shi zuwa ga kasasahe 10 dake a Afirka.

Ya ce, kamfanin masana’antu nika simintin a kasashe bakwai da suka hada da, Kamaru tare da kayan rabar da shi masana’antar sa da ke a Ghana da Sierra Leone, inda daukacin wannan, ya sa kamfanin ke akan gaba wajen sarrafa simitin a daukacin naihyar Afirka.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here