UEFA za ta biya magoya bayan Liverpool kudin tikitin su

0
70

Hukumar kwallon kafa ta kasashen turai UEFA, za ta biya kudin tikitin magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, wadanda suka saya don kallon wasan karshe na Champions League a birnin Paris a shekarar da ta gabata ta 2022.

Hakan ya biyo bayan wani kwamiti mai zaman kansa da ya binciko cewar UEFA ce ta haddasa turmutsitsin da ya faru, kafin wasan karshe tsakanin kungiyar Liverpool da Real Madrid.

Magoya baya da dama ba su samu damar shiga kallon wasan ba, an kuma bada barkonon tsohuwa a fafatawar da aka yi lattin minti 36 kafin fara wasan saboda matsalar da aka samu.

UEFA ta ce za ta biya dukkan tikiti dubu 19, 618 da aka bai wa magoya bayan Liverpool, domin kallon fafatawar da aka yi a Faransa kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa tuni aka fara biyan magoya bayan.

Real Madrid ce ta ci Liverpool 1-0 ta dauki Champions League na 14 jimilla kuma a kakar nan kungiyoyin sun buga a Ingila a zagayen ‘yan 16 a gasar zakarun Turai, inda Real Madrid ta ci Liverpool 5-2 a filin wasa na Anfield ranar 21 ga watan Fabrairu.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Liverpool a wasa na biyu ranar 15 ga watan Maris a Santiago Bernabeu sai dai a wannan karon Liverpool, za ta je Sifaniya da kwarin gwiwa, bayan da ta doke Manchester United 7-0 ranar Lahadi a Premier League a Anfirld.

Ita kuwa Real Madrid, waddaa Barcelona ta bawa tazarar maki tara a teburin La Liga, ta je ta tashi 0-0 da Real Betis ranar Lahadi kuma wasa na uku kenan kungiyar ba ta samu nasara ba a jere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here