Dikko Radda na APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina

0
43

Hukumar zaben Najeriya INEC ta ayyana Dokta Umar Radda na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Katsina.

Radda ya samu nasara ne da ƙuri’u 859,892, yayin da mai biye masa Garba Yakubu Lado Danmarke na jam’iyyar PDP ya samu kuri’a 486,620.

Jami’in da ke tattara sakamakon zaɓen gwamnan a jihar ta Katsina, Farfesa Mu’azu Abubakar Gusau ne ya bayyana sakamakon a daren Lahadi.

Jihar Katsina ita ce jihar shugaban Najeriya Muhammad Buhari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here