Amurka ta na barazanar ladabtar da Uganda saboda dokar hukunta masu luwaɗi

0
44

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta yi gargaɗin cewa za ta hukunta Uganda ta fannin tattalin arziƙi matuƙar aka tabbatar da dokar tsananta wa masu neman jinsi ɗaya.

Mai magana da yawun majalisar tsaron Amurka, John Kirby ya shaida wa manema labaru cewar “za mu duba mu ga wane mataki za mu ɗauka, kamar ta ɓangaren tattalin arziƙi, matuƙar aka amince da fara aiki da dokar.”

“Saboda haka za mu duba. Har yanzu ba mu ɗauki mataki ba, amma muna lura da duk abin da ke gudana. Muna fatan cewa ba za a amince da dokar ba, mu ma shi ke nan ba sai mun ɗauki mataki ba.”

Dokar dai ta tanadi hukuncin ɗaurin rai-da-rai a kan mutanen da suka bayyana kansu a matsayin ƴan luwaɗi a Uganda. Haka nan kuma zai iya kai wa ga hukuncin kisa.

Yanzu haka dokar na jiran amincewar shugaban ƙasa domin ta fara aiki.

Tarayyar Turai ma ta nuna damuwarta game da sanya hannu kan dokar.

EU ta ce “Tarayyar Turai za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomi da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma ɗaiɗaikun mutane a Uganda, domin ganin cewa ana ɗaukar kowa a matsayi guda, da girmama mutane ba tare da la’akari da irin rayuwar da suke so su yi ba, ko kuma jinsinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here