Majalisar dattawa zata kafa hukumar da zata tallafawa talakawa zalla a Najeriya

0
72

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da ayyuka na musamman ya yi alwashin yin doka da zata taimaka wajen kafa wata hukuma da zata kyautata wa talakawa da masu karamin karfi, to sai dai masana na ganin akwai abin dubawa domin sauran hukumomin da ake da su ba a tafiyar da ayyukansu yadda yakamata.

Wannan doka dai idan aka yi ta zata tabbatar da dorewar shirin nan na gwamnatin tarayya na tallafa wa marasa karfi da gajiyayyu maza da mata a Najeriya wanda aka fara a shekarar 2016. Shugaban Kwamitin Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, shi ne ya sanar da haka a lokacin taron jin ra’ayoyin jama’a kan kudurin dokar da zata tabbatar da hukumar.

Yusuf ya ce an gabatar da kudurin ne domin ana so a bar wani muhimmin abu bayan wa’adin gwamnati mai ci, saboda an ga alfanun shirin wanda aka kwashi shekaru kusan bakwai ana yi kuma mutane suna samun tallafi.

Yusuf ya ce abu ne mai kyau idan gwamnati mai jiran gado zata ci gaba da shi, shi ya sa za a yi dokar da zata karfafa mata gwiwa ganin cewa aikin gwamnti ne tallafa wa talakawan kasa.

Shugaban shirin tallafa wa talakawa na kasa Dr. Umar Buba Bindir, ya ce mutane da yawa sun amfana da shirin.

An kasa shirin zuwa bangarori hudu, da farko akwai matasa miliyan daya da dubu dari biyar wadanda basu da aiki, ana koya masu sana’a sannan a basu tallafi.

Akwai kuma yaran talaka da ake ciyar wa a makarantu su miliyan goma zuwa miliyan sha biyu, da mata miliyan uku masu kananan sana’o’i da ake basu bashin kudi dubu hamsin zuwa dubu dari uku, sannan akwai gidaje miliyan biyu da ke dauke da mutane miliyan goma da ake ba su naira dubu 5 domin su samu abinci.

Bindir ya ce shiri ne da ya kamata ya dore amma a karkashin hukuma mai zaman kanta.

To amma ga Kwararre a fannin tattalin arziki Yusha’u Aliyu, ya na ganin kafa hukuma a yanzu ba daidai ba ne.

Yusha’u ya ce tun bayan da aka samu ‘yancin kai an yi ta kokarin kafa hukumomi da zasu taimaka wa talakawa amma ba a taba samun inda talakawa suka yi yawa irin yanzu ba.

Yusha’u ya ce yanzu talakawan Najeriya sun kai miliyan dari da talatin da uku, a saboda haka yana ba ‘yan majalisa shawara kan su mayar da hankali akan tsare-tsaren da ke dora yawan haraji a kasa, kuma ba a ganin inda kudaden suke shiga, don haka suka kafa kwamiti da zai kawo hanyoyin raya tattalin arzikin kasar.

Abin jira a gani shi ne irin tasirin da dokar za ta yi idan majalisa ta kafa ta, duk da cewa shugaban kwamitin Sanata Yusuf Abubakar Yusuf, ya tabbatar cewa bangaren gwamnati sun nuna goyon bayansu ga kudurin dokar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here