Zamfara: ‘Yan sanda sun bi umarnin kotu, sun mayarwa da Matawalle motocinsa

0
83

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara a ranar Asabar din da ta gabata ta ce ta mayar da dukkan motocin da ta kama daga hannun tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Yazid Abubakar ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, hakan a ranar Asabar ta wayar tarho.

Abubakar ya ce an mayar da motocin ne bisa bin umarnin babbar kotun tarayya da ke Gusau.

Kotun karkashin jagorancin Mai shari’a Aminu Bappah-Aliyu, ta bayar da umarnin a ranar 15 ga watan Yuni, ta umurci dukkanin jami’an tsaron da suka kwashe motocin daga gidajen Matawalle da ke Gusau da Maradun, da su dawo da su cikin sa’o’i 48.

NAN ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun kwashe motocin daga gidajen biyu bisa umarnin gwamnatin jihar.

Kotun ta bai wa duk wanda ke da hannu a harin da aka kai wa gidajen tsohon gwamnan wa’adin sa’o’i 48 domin su bi wannan umarni.

“Eh, rundunar ‘yan sanda ta bi umarnin kotu dangane da mayar da dukkan motocin tsohon gwamna Bello Matawalle.

“Mun mayar da dukkan motocin zuwa harabar babbar kotun tarayya da ke Gusau, kamar yadda nake magana da ku a yanzu, babu wata mota guda da ke hannun ‘yan sanda,” in ji Abubakar.

Kotun ta kuma bayar da umarnin dakatar da wadanda ake kara a karar da Matawalle ya shigar a gaban kotu daga daukar wani mataki na gaba dangane da lamarin.

Wadanda suka amsa sun hada da Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya da kuma kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara.

Sauran sun hada da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da kuma NSCDC na Nigeria Security and Civil Defence.

Kotun ta kuma umarci jami’an tsaro da su nisanta kansu daga duk wani mataki da za a dauka, har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci a gabanta.

Mista Suleiman Idris, mai magana da yawun Gwamna Dauda Lawal na Zamfara, a baya ya ce an kwato motoci fiye da 40 a gidajen tsohon gwamnan biyu.

Ya kuma tabbatar da cewa hukumomin tsaro sun dauki matakin ne bisa umarnin gwamnatin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here