Damuwar da ‘yan Nijar mazauna Najeriya suka shiga kan wa’adin Ecowas

0
106

Ana cike fargaba da zaman ɗar-ɗar bayan cikar wa’adin da Ecowas ta bai wa sojojin Nijar, na su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar, Mohamed Bazoum ko kuma su fuskanci yiwuwar ɗaukar matakin sojoji daga ƙungiyar ƙasashen.

Ranar waccan Lahadin ce shugabannin Ƙasashen Afirka ta Yamma suka bai wa masu juyin mulkin wa’adin mako ɗaya a kan su yi biyayya ga buƙatunsu ko kuma su “ɗauki dukkan matakai… [waɗanda] suna iya haɗar da amfani da ƙarfi”.

Sai dai a maƙwabciyar Nijar, Najeriya – inda da yiwuwa sojojin da za a tura Nijar masu yawa za su fito – amon masu nuna adawa da ɗaukar matakin soji yana daɗa ƙarfi.

Wasu ‘yan Nijar mazauna jihar Sokoto a Najeriya sun faɗa wa BBC irin fargabar da suka shiga. 

Ƙasashen biyu na da alaƙa ta kusancin al’umma da kuma tarihi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here