Tinubu ya kafa kwamitin garambawul a harkar tara haraji

0
146

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da wani kwamiti da zai yi garambawul a harkar tara haraji da manufofin kuɗi, a yunƙurinsa na ganin haraji ya zama kashi 18% na arziƙin da Najeriya ke samu cikin duk abin da ta sarrafa a gida, wato GDP, nan da shekara uku. 

Shugaban ya ce matakin zai taimaka wajen ganin Najeriya ta rage dogaro a kan bashi wajen samun kuɗin gudanar da harkokin gwamnati. 

Wata sanarwa da mashawarcin shugaban Najeriyar na musamman kan harkar yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar ta ambato Tinubu na umartar shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele, ya yi nazari don gyaran fuska a harkokin kuɗi da garambawul a harkar tara haraji da kuma kyautata bunƙasar tattalin arziƙi a cikin shekara ɗaya.

Tinubu ya ce Najeriya har yanzu tana fuskantar ƙalubale a ɓangarorin da suka haɗar da biyan haraji cikin sauƙi, kuma kason haraji da take karɓa idan an kwatanta da kuɗin da take samu daga duk abin da ta sarrafa a gida ya yi kaɗan. A cewarsa ƙasar, ta zama kurar baya a Afirka a wannan ɓangare. 

Sanarwar ta ce manufar shugaban ƙasar ita ce yi wa tsarin karɓar haraji gyaran fuska don tallafa wa bunƙasa harkokin ci gaba mai ɗorewa. 

Ya ce matuƙar babu kuɗin shiga, gwamnati ba za ta iya samar isassun ayyukan inganta rayuwa ga al’ummar da suka ba ta amana ba. 

Shugaba Tinubu ya ba da umarnin cewa ana sa ran kwamitin zai gabatar da wani tsarin garambawul cikin gaggawa da za a iya aiwatarwa a cikin kwana 30. Sai kuma ba da shawarwari kan muhimman sauye-sauye a cikin wata shida, aiwatar da cikakkun tsare-tsaren a cikin shekara ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here