‘Yan sanda sun cafke kasurgumin dan bindiga a Jigawa

0
93

Rundunar ‘yansandan Jihar Jigawa ta cafke wani mutum mai suna Abdulkadir Alhassan mai shekaru 42 da haihuwa wanda ya dade yana ta’addanci a jihar da kuma Jihar Kano.

Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Lawan Shiisu Adam, ne ya tabbatar da kamen a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Talata a kauyen Sabon Sara da ke karamar hukumar Ringim.

Shiisu ya bayyana cewa wanda ake zargin kasurgumin dan fashi da makami ne kuma mai garkuwa da mutane wanda aka gurfanar da shi a gaban kuliya bisa laifukan fashi da makami.

“Wanda ake zargin an bada belinsa kwanan nan a kan laifin hada baki da kuma aikata fashi da makami a kotun majistare Babura,” in ji shi.

Ya ce wanda ake zargin ya amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama daga jihohin Jigawa da Kano.

Yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa laifin karbar miliyoyin Naira daga iyalan wadanda abin ya shafa a matsayin kudin fansa.

Kakakin ‘yansandan ya kara da cewa wadanda ake zargin ya bayyana sunan wani dan kungiyarsu mai suna Alhassan Ya’u dan shekaru 45 a kauyen Dogamare da ke karamar hukumar Ringim.

Za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike.