EFCC ta kama ma’aikatan banki 12 kan satar kudin kwastomomi

0
79

Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC), ta cafke wasu ma’aikatan banki 12 kan zargin wawure kudaden kwastomominsu daga asusunsu na ajiya.

Rahotanni sun bayyana cewa ababen zargin sun shiga hannu ne tun a ranar Juma’a 14 ga watan Oktoban da muke ciki.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Asabar, ya bayyana sunayen ma’aikatan bakin 12 da ake zargi da aikata wannan zamba a Jihar Enugu.

Hukumar ta ce binciken farko dai ya nuna ababen zargin sun sace kudaden ne daga asusan ajiyar abokanan huldarsu wadanda suka dade ba a yi amfani da su ba.

Sanarwar ta ce ma’aikatan bankin sun wawure kudaden ne daga asusan ajiyar kwastomomi daban-daban.

Mista Uwujaren ya ce za a gurfanar da ababen zargin a gaban Kuliya da zarar sun kammala bincike.