Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da ofishin yakin neman zabensa a Kano

0
61

Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya kaddamar da ofishin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC a birnin Kano.

da yake kaddamar da ofishin a ranar Asabar a Kano, ya ce ofishin ya cika tsarin yakin neman zabe ya, kuma ya bayyana fatansa na ganin APC za ta yi nasara a dukkan matakai a babban zaben 2023 mai zuwa.

” Bola Ahmad Tinubu yace ya gamsu da abin da ya gani game da shirye-shirye da kungiyoyin tsarin yakin neman zabe a nan kano,”

Tinubu ya ce ba ya je Kano ne ba don yakin neman zabe ba kawai, sai dan ya kaddamar da ofishin yakin neman zabe da kuma duba shi.

Dan takarar na jam’iyyar APC ya tabbatar da cewa idan har aka zabe shi a kan karagar mulki, zai ciyar da kasar nan gaba, kuma ‘yan Nijeriya ba za su yi nadamar zaben sa ba.

“Za mu yi amfani da tsintsiya madaurinki daya domin tsaftace kasar da kuma baiwa ‘yan Najeriya farin ciki,” in ji shi.

Tinubu, wanda ya jaddada mahimmancin mata a cikin al’umma, ya ce suna da muhimmiyar rawar da za su taka domin samun nasarar jam’iyyar a babban zabe.

Tun da farko Gwamna Abdullahi Ganduje ya bada tabbacin cewa al’ummar jihar za su kada kuri’a ga jam’iyyar APC kamar yadda suka saba.

“Kano APC ce, APC kuma Kano ce. Don haka mutanenmu suna cikin jirgin kuma muna neman goyon bayansu kamar yadda muka saba,” inji shi.

Ganduje ya ce Tinubu shugaba ne da zai hada kan al’umma gaba daya.

Shima da yake jawabi, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sen. Abdullahi Adamu, ya ce jam’iyyar ba ta da hujjar gazawa idan aka yi la’akari da farin jininta da yawan gwamnoni.

Ya bukaci daukacin ‘yan Najeriya, ba tare da la’akari da kabila ko addini ba, da su marawa Tinubu da duk ‘yan takarar jam’iyyar APC goyon baya domin ci gaban kasa baki daya.

Gwamnonin jihohin Kano, Jigawa da Zamfara, Abdullahi Ganduje, Alhaji Badaru Abubakar da Alhaji Bello Matawalle ne suka tarbi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.

Tinubu wanda ya samu gagarumar tarba daga al’ummar Kano, ya kuma duba ofishin kwamitin gudanarwa na jam’iyyar APC da ke Audu Bako way da Zariya road bi da bi.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC zai kuma kai ziyarar ban girma ga mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado tare da ganawa da sarakunan Gaya da Rano da Bichi da kuma Karaye a ranar Lahadi.