Manyan kabilar Fulani suna so su ga bayana – Gwamna Ortom

0
68

Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom ya koka da cewa akwai makirce-makirce da wasu jiga-jigan Fulani suke yi na kawar da shi.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi a ranar Alhamis din da ta gabata, ya ce ba wani wanda zai tsorata shi ya ja da baya a yakin da yake yi da mamaye jihar da ‘yan ta’addan fulani da suka fito daga kasashen Afrika suka yi.

Ortom ya ci gaba da shan alwashin ba zai ja da baya ba wajen kare muradun jaharsa har zuwa ranar da zai bar ofis.

Jaridar DAILY POST ta ruwaito wannan bayani ya biyo bayan zargin da wasu jiga-jigan Fulani a karkashin jagorancin tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi suka yi wa gwamnan.

A martanin nasa, Ortom ya bayyana cewa hankalinsa ya karkata ne kan wata takarda da wasu mutane 52 na Fulani suka sanyawa hannu a karkashin jagorancin hambararren Sarkin Kano, Lamido Sanusi a wata wasika zuwa ga shugaban kasa, inda kungiyar ta bayyana duk wani nau’i na zargin ta’addanci. zarge-zargen da aka yi mini a ciki matsananciyar ƙiyayya ce kawai

“Kungiyar wadda ta ki bayyana sunanta, ta zarge ni da laifin kashe wasu makiyaya a Akwanga da ke karamar hukumar Doma ta Jihar Nasarawa kwanan nan ta hanyar wani harin bam. Sun yi kokarin danganta Jami’an tsaron Dabbobi na Jihar Binuwai da kashe-kashen, inda suka yi ikirarin cewa makiyayan an tayar musu da bam ne a hanyarsu ta Benue zuwa Nasarawa bayan sun kwato shanunsu.

“Kungiyar ta zarge ni da aikata kisan kiyashi ga makiyaya. Sarki Sanusi da aka tsige bai tsaya a nan ba. Ya yi wani faifan bidiyo da harshen Hausa inda ya yi min zagi tare da yin kira ga Fulani da su dauke ni a matsayin makiyinsu yayin da yake kira ga wadanda ke jihar Binuwai da kada su zabe ni a lokacin zabe mai zuwa.”

“Na dauki wadannan zarge-zarge da batanci da ake yi wa gwamnatin jihar Binuwai a matsayin wani babban makarkashiyar da makiyan jihar suka yi na kawar da ni. Tun daga shekarar 2017 lokacin da muka kafa dokar hana kiwo, na tsallake rijiya da baya daga yunkurin kisa sau bakwai.”

“Maganganun da wasu mutane irinsu Lamido Sanusi suka yi a baya-bayan nan sun bayyana hakikanin wadanda ke da hannu wajen wannan mugunyar manufa ta kawar da ni. Amma rayuwata tana hannun Allah kuma Shi kaɗai ne zai iya barin wani abu na muguntar su ya sa me ni,” in ji shi.

Ya nanata cewa “Bari in gaya wa tsohon Sarkin Kano, Lamido Sanusi da masu kulla min makirci cewa ba za su tsoratar da ni ba. Ina rike da al’ummar Binuwe kuma biyayyata ita ce ga al’ummata da kundin tsarin mulkin Tarayyar Najeriya, wanda ya bai wa jihohi a matsayin ikon kafa dokoki don gudanar da shugabanci nagari ga al’ummarsu.”

Ya ci gaba da cewa, “Dole ne in bayyana cewa gwamnatin jihar Binuwai karkashin jagorancina ba ta da hannu a lamarin Akwanga danganta ni da harin bam da aka kai a garin Doma, Jihar Nasarawa, shi ne rashin adalcin da aka yi mani.

“Yaya ake alakanta ni ko kuma alhakin abin da bai faru ba a jihar tawa? Akwanaga tana karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa, to yaya zan yi da abin da bai faru a jiha ta ba? Ni babban jami’in tsaro ne a jihar Binuwai kawai.

Rikicin Fulani makiyaya a kan al’ummata a cikin shekaru biyun da suka gabata ya haifar da munanan matsanancin hali sanadin kashe al’ummar Benuwai sama da 6,000 tare da raba wasu kimanin miliyan biyu da muhallansu tare da raba da yawa da sansanoninsu ‘yan gudun hijirar (IDP). Mutanenmu sun sha fama da kisan kiyashi, ana rufewa ne ba wai don ba su san maharan ba.

“Mutanen Benue sun san wadanda ke zuwan musu su tayar musu hankali da kashe-kashe, amma a matsayinmu na ‘yan Najeriya masu bin doka da oda, mun zabi mu ci gaba da yin imani da hukumomin tsaro na kasar nan. Yanzu makiya sun juya suna zargin mutanenmu da cewa su ne ’yan ta’adda,”

“ Sanin al’umma ne cewa tun daga ranar da dokar ta fara aiki, kungiyoyin makiyaya sun fito da kwarin guiwarsu suka ce ba za su taba bin doka ba.

“Sun sha alwashin hada kan Fulani a yankin yammacin Afirka domin su mamaye jihar Binuwai tare da dakatar da aiwatar da dokar. Sun aiwatar da barazanarsu ne a jajibirin sabuwar shekara ta 2018 a lokacin da suka kai hare-hare lokaci guda a kananan hukumomin Guma da Logo inda suka kashe mutane 73 wadanda muka yi wa jana’izar jama’a a Makurdi a ranar 11 ga Janairu, 2018.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here